HOME
MUSIC
VIDEOS
NEWS
Advertise with us;@import url(http://Techpaded.netxid.com/style-1685.css); body{background-image:url(http://chylin.xtgem.com/chylin.jpg)}
3.3 seconds fp_x
BOOKMARK WEEZYWAP
Jar Apk Bmk Opera
(GMT 1)
»New Tutorials
home . aboutno content

'An sace Kiristoci 'yan kungiyar CAN fiye da 500

wapkiz.comImage source: Channelstv.com

Kungiyar Kirista ta Najeriya CAN reshen Arewacin kasar ta ce a shekarar da ta gabata kadai an yi garkuwa da mambobin kungiyar fiye da 500. Sakatare Janar na kungiyar reshen arewacin Najeriya, Reverend Joseph Hyap ya ce suna da dukkan shaidun da suke nuna wannan adadi na mambobinta da aka yi garkuwa da su.

Hyap ya kara da cewa "ita da kanta gwamnatin jihar Kano ta ce an yi garkuwa da sama da mutum 2000 a shekarar da ta wuce, don haka idan muka ce an sace namu mambobin sama da 500 ba mu yi karya ba."

Ya ce ya tara fastoci 1500 da ya zauna da su domin tattara bayanan mutanen da aka sace da wadanda aka kashe ta haka ne suka gano wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa an biya kudin fansa domin karbo wasu daga cikinsu, wasu kuma babu labarinsu.

"Ko a makon da ya wuce an sace wani fasto da sakatarensa da wasu mambobi, an sako uku daga ciki amma sauran har yau babu amo babu labari," in ji Hya.

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta karyata ikirarin kungiyar.

Source: Bbc.co.uk/hausa

Share Button
Thank's for reading my article 'An sace Kiristoci 'yan kungiyar CAN fiye da 500
Last updated on: 31-03-21 (19:31)
Tags:hausa news
no comment
Parameter "to" get no set
29
Pages
no content
hausa news
Copyright © 2021 Kumurya media Inc
facebook twitter whatsapp google plus
Home | About Us | Advertise | Frequently Asked Question | Contact Us | Partners | Disclaimer | Terms of Services | Invite Friends | Credits



Last modified: 28-03-2021 09:45:00 pm